in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta shigar da masu shiga tsakani na kasashen waje cikin fafutukar kubutar da 'Yan matan Chibok
2017-04-14 09:47:15 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ta shigar da masu shiga tsakani na gida da ketare, a kokarin da take na ganin kungiyar Boko Haram ta saki 'yan matan sakandaren Chibok dake hannunta.

Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana haka a jawabin da ya yi na cika shekaru 3 da sace 'yan matan a ranar 14 ga watan Afrilu, ya ce gwamnatinsa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin wadanda suka sace 'yan matan sun sake su.

Ya ce 'yan Nijeriya suna da hujjar yin murnar dawowar 24 daga cikin 'yan matan, tare da sauran dubban mutane da mayakan kungiyar suka sace.

Ya ce gwamnati ta na ci gaba da kokari ta hanyar kulla yarjejeniya da kuma bayanan hukumomin tsaro na farin kaya, don ganin an saki sauran 'yan matan da mutanen da aka sace.

Shugaban kasar, ya kuma roki iyayen yan matan da sauran 'yan Nijeriya, kada su yanke kaunar sauran za su dawo.

A daren ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne mayakan kungiyar Boko Haram, suka yi wa dakunan baccin 'yan matan sakandaren Chibok dirar mikiya, inda suka yi awan gaba da 'yan mata sama da 200. Wasu daga cikinsu sun tsere, sai dai, har yanzu ba a san inda sauran suke ba.

A kuma ranar 13 ga watan Oktoban bara ne, aka saki 21 daga cikin 'yan matan, bayan wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin gwamnatin Nijeriya da kungiyar Boko Haram da ta dauki alhakin sace su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China