Ministar al'amurran mata ta Najeriyar Aisha Alhassan, ita ce ta shigar da 'yan matan fadar shugaban kasar cikin wasu fararen motoci biyu mallakar sojojin Najeriyar.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ce motoci na da tagogi masu duhu ta yadda ba za'a iya gane fuskokin 'yan matan ba.
A ranar Asabar din da ta gabata ne, aka sako 'yan matan, bayan cimma yarjejeniya da mayakan 'yan tada kayar baya.
Ya zuwa yanzu, 'yan matan sakandaren Chibok 103 ne aka yi nasarar ceto su daga hannun mayakan na Boko Haram.
An ceto kashin farko na 'yan matan 21 ne a watan Oktoban shekarar da ta gabata bayan da kasar Switzerland da kungiyar Red Cross suka shiga tsakani domin yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya da mayakan na Boko Haram. Da ma dai wasu 'yan matan biyu sun yi nasarar kubutar da kansu, inda yawan 'yan matan da suka tsira daga hannun Boko Haram ya tasamma 105.
A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne aka sace 'yan matan sama da 200 a makarantar sakandaren 'yan matan dake garin Chibok, lamarin da ya tada hankalin al'ummar Najeriya da ma kasashen duniya baki daya.
A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015 gwamnatin shugaba Buhari ta fara jan ragamar shugabancin Najeriya, kuma tun daga wancan lokacin gwamnatin Buhari take daukar matakai iri daban daban domin ceto 'yan matan da ransu.
Da ma dai shugaba Buhari ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ceto ragowar 'yan matan da ake tsare da su, a lokacin da ya aike da sakonsa a bikin cika shekaru 3 da sace 'yan matan na Chibok.(Ahmad Fagam)