Kasar Sin za ta iya samar da daidaituwar al'amurran kudi, ci gaban tattalin arziki sannu a hankali, da kuma bunkasuwar tattalin arziki, Li ya bayyana hakan ne a lokacin ganawar da manajar daraktar asusun bada lamini na duniya wato (IMF) Christine Lagarde, wacce a halin yanzu take nan birnin Beijing domin halartar taron kasa da kasa na "ziri daya hanya daya".
A cewarsa, gwamnatin za kuma ta ci gaba da hada hada a fannin kasuwannin kudi, domin tabbatar da kiyaye tsarin musayar kudi domin daidatuwar darajar kudin kasar yuan a mataki mafi dacewa.
Kasar Sin a shirye take ta karfafa tsarin tuntuba da gudanar da al'amurra da bankin bada lamini na IMF, ta yadda za'a iya samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da kasuwanci da zuba jari mai cike da yanci da harkokin gudanarwa, har ma da hadin gwiwa a bangarori da dama, domin kiyaye makomar tattalin arzikin duniya don ya tsaya da gindinsa, inji Mista Li.
A nata bangaren Lagarde, ta bayyana cewa, cigaban da kasar Sin ke samu a halin yanzu babban abin karfafa gwiwa ne. Ta kuma yabawa kasar game da kokarin da take yi na tabbatar da hadin gwiwar kasa da kasa da nufin samar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya da harkokin kasuwanci na bangarorin duniya daban daban. (Ahmad Fagam)