Ya zuwa karshen shekarar 2017, kasar Sin za ta kammala aikin samar da sabbin gidaje miliyan 18 da ta fara aikinsu cikin shekaru 3 karkashin shirin bunkasa birane a duk fadin kasar.
Wannan batu, an gabatar da shi ne a lokacin zaman majalisar gudanarwa ta kasar Sin wanda firaiminista Li Keqiang ya jagoranta a jiya Laraba.
Li ya bukaci a kara kokari wajen aiwatar da shirin kamar yadda aka tsara tun da farko. Kana ya bayyana wannan shiri a matsayin wani muhimmin garambawul na inganta yanayin zaman rayuwar al'ummar kasar.
Ya ce, hukumomin kasar sun nuna jajurcewa matuka cikin shekaru 8 da suka gabata, kuma wannan yunkuri nasu ya haifar da kyakkyawan sakamako da ake son cimmawa.
A cewar ma'aikatar samar da gidaje da raya birane da karkara, gwamnatin ta zuba tsabar kudi da ya kai yuan triliyan 1.48 kwatankwacin dala biliyan 215.25 daga shekarar 2016, domin gina sabbin gidaje miliyan 6.06 ga mutanen dake zaune a gidaje na wucin kadi, an samu karin gidaje sama da 60,000 idan aka kwatanta da adadin da aka kuduri aniyar samarwa. A shekarar 2015, adadin gidajen ya kai miliyan 6.01.(Ahmad Fagam)