An bukaci manyan bankunan kasuwanci na kasar Sin da su kafa wani sashen tattara kudade wadanda za'a yi amfani da su don tallafawa kananan masana'antu, da aikin gona, da rage radadin talauci da sana'o'in hannu a wannan shekarar ta 2017.
A wata sanarwa da firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar a lokacin da ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar, ya ambata cewa, ya kamata manyan bankunan kasar su kasance kashin bayan ci gaba ta fuskar samar da kudade.
Sanarwar ta kara da cewa, idan manyan bankunan kasar suka samar da rance ga kananan kamfanoni da masana'antun kasar, hakan zai yi matukar tasiri wajen samun bunkasuwa.
Mista Li Keqiang ya ce, ya kamata bankunan su ba da muhimmanci ga sha'anin samar da rancen kudaden wajen bunkasa kananan masana'antu, da aikin gona, da kawar da talauci.(Ahmad Fagam)