An labarta cewa, an kafa kamfanin BAIC MOTOR reshen Zimbabwe ne a karkashin hadin-gwiwar wani hamshakin kamfanin kera motoci na birnin Beijing, da wadansu kamfanonin kera motoci na Zimbabwe guda biyu.
Bisa yarjejeniyar da suka cimma, wannan kamfani zai samar da guraban ayyukan yi kimanin dubu biyar a wurin, da kera motoci dubu daya a bana, matakin da zai kawowa Zimbabwe kudin haraji da yawansa zai kai dala miliyan 1.3.(Murtala Zhang)