Taken bikin a wannan karo shi ne "kyautata yanayin yin ciniki don bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma". A gun bikin, shugaba Mugabe ya duba faretin sojojin kasar tare da yin wani jawabi.
Kasar Zimbabwe za ta gudanar da zaben shugaba da majalisar dokoki da kananan gwamnatocin kasar a shekara mai zuwa. Ko da yake ba a tabbatar da lokacin zaben ba, amma jam'iyyu daban daban sun riga sun fara yakin neman zaben.
Kafin hakan, jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar Zimbabwe wato Zanu-PF ta sanar da cewa, shugaban kasar na yanzu Mugabe mai shekaru 93 da haihuwa zai zama 'dan takarar jam'iyyar a zaben shugaban kasar na shekarar 2018. Idan ya cimma nasarar zaben, zai zama shugaban kasar har zuwa lokacin da shekarunsa za su kai 99 a duniya. (Zainab)