in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya gargadi mahukuntan Zimbabwe game da kashe kudade barkatai
2017-05-17 10:36:01 cri
Asusun ba da lamuni na IMF, ya gargadi mahukuntan kasar Zimbabwe, game da kashe kudade barkatai, kasancewar hakan na iya haddasa karancin kudade, da hauhawar farashin mai a kasar.

Wata sanarwa da IMF ya fitar a jiya Litinin, bayan ran gadi da jami'an sa suka kai kasar makwanni biyu da suka gabata, ta rawaito jagorar tawagar Ana Lucia Coronel, na bayyana irin matsi da kasar ke fuskanta, wanda hakan ya sanya IMF din baiwa mahukuntan Zimbabwe, shawarar inganta wasu sassan tattalin arzikin kasar.

IMF ya ce, ya dace Zimbabwe ta dakile matsi a fannin tattalin arziki sakamakon tsadar kwadago, da bukatun dake bullowa sakamakon fatan inganta zamantakewar alumma, da ma sauran bukatu na kashe kudade.

Kaza lika IMF ta shawarci Zimbabwe da ta fadada fannin tattalin arziki a sassa masu zaman kan su, tare da tabbatar da marasa karfi na cin gajiya daga irin wadannan sassa.

A daya bangare kuma, IMF na ganin lokaci ya yi da mahukuntan Zimbabwe za su dora inda aka tsaya, game da bude kofofin su ga masu zuba jari. Hakan a cewar wannan sanarwa ya kunshi daukar matakan yaki da cin hanci da rashawa, da karfafa gwiwar masu zuba jari a sassan da ba na gwamnati ba, da barin kasuwa ta yi halinta, da hore damar gudanar da gwadago cikin 'yanci, da kuma samar da dokoki da za su rage rashin tabbas a fannin tsare tsaren hukuma.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China