in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 246 a Zimbabwe
2017-03-03 11:02:59 cri
Wani jami'in gwamnatin kasar Zimbabwe ya bayyana jiya Alhamis cewa, an fuskanci bala'in ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasar, sakamakon ruwan saman da aka sheka kamar da bakin kwarya a kwanakin nan, al'amarin da ya yi sanadiyyar halaka mutane akalla 246, baya ga wasu mutane sama da dubu biyu da suka bar muhallansu.

Alkaluman na nuna cewa, ya zuwa yanzu ambaliyar ruwar ta rushe gidaje 2579, da makarantu 74 gami da cibiyoyin samar da jinya guda biyar, baya ga dabbobin gida da dama da suka mutu sakamakon wannan bala'i. A kwanakin baya ne, gwamnatin kasar Zimbabwe ta ayyana yankin kudancin kasar, wanda matsalar ta fi shafa, a matsayin yanayin ko-ta-kwana.

Ministan kula da harkokin kananan hukumomi na Zimbabwe Saviour Kasukuwere ya ce, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka tun daga watan Nuwamban bara har zuwa yanzu, ruwan dake cikin akasarin wuraren adana ruwa na kasar ya wuce mizanin gargadi. Ministan ya kuma yi kira ga kasashe daban-daban da su tallafawa mutanen da bala'in ya shafa.

A nata bangaren kuma, ministar kula da harkokin muhalli ta Zimbabwe Madam Oppah Muchinguri ta ce, ruwan sama mai tsanani ya lalata na'urorin adana ruwa da dama a Zimbabwe, a halin yanzu, akwai 'yan kasar sama da dubu dari wadanda ba sa iya samun tsaftaccen ruwan sha.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China