in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan bindiga sun hallaka kiristoci 26 a Masar
2017-05-26 20:01:43 cri

A kalla wasu mabiya addinin kirista 26 ne suka rasa rayukan su, kana wasu 25 suka jikkata a Juma'ar nan, sakamakon hari da wasu 'yan bindiga suka kai masu a lardin Minya dake kudancin kasar Masar.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun budewa motar da mutanen ke ciki wuta, lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa majami'a. Tun da fari dai 'yan bindigar sun tsare motar kirar bas wanda a lokacin dake kan hanyar ta zuwa wurin idaba na Samuel dake kudancin birnin Alkahira, kafin su yiwa mutanen dake cikin motar harbin kan mai uwa da wabi.

Tuni dai aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin lardin Minya. Kaza lika jami'an tsaron kasar sun killace wurin da lamarin ya auku, yayin da kuma suke ci gaba da farautar wadanda suka aikata wannan ta'asa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China