in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Masar sun gano maboyar yan ta'adda a tsakiyar birnin Sinai
2017-05-14 11:49:05 cri
Mai magana da yawun dakarin sojin kasar Masar Tamer al-Refaay, ya bayyana cewa, sojin kasar sun bankado wata maboyar yan ta'adda wadda ke dauke da manyan makamai da abubuwan fashewa a tsakiyar birnin Sinai.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na runduna ta uku na kasar na cigaba da yin lugudan wuta kan maboyar yan ta'addan a daidai lokacin da kasar ke fafutukar murkushe yan ta'adda daga tsakiyar birnin na Sinai.

Hare haren da masu adawa da gwamnatin kasar Masar suka kaddamar ya yi sanadiyyar rayukan daruruwan sojoji da yan sandan kasar tun daga shekarar 2013 tun bayan kifar da gwamnatin shugaban kasar Mohamed Morsi sakamakon mummunan zanga zangar nuna adawa da mulkinsa na tsawon shekara guda.

Mafi yawan hare haren ta'addanci da aka kaddamar musamman a birnin Sinai, kungiyoyin yan ta'adda mazauna Sinai wadanda ke yin biyayya ga kungiyar IS ne suke daukar alhakinsu.

Dakarun wanzar da zaman lafiya dake Sinai sun yi nasarar karkashe daruruwan mayakan yan ta'addan, kuma sun damke wasu da dama a shekarun da suka gabata, a matsayin wani shiri na yaki da ta'addaci wanda shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya kadda bayan hambare Morsi. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China