Kwamitin ya kuma kalubalanci dukkan kasashe su hada kai da Masar wajen yaki da ayyukan ta'addanci bisa dokokin kasa da kasa da kudurorin kwamitin sulhun.
Shi ma a nasa bangare, Antonio Guterres ya bayar da sanarwa ta bakin kakakinsa cewa, babu wani dalili da zai sa a kai irin wannan farmaki na ban mamaki.
Ya kuma nuna juyayi tare da jajantawa iyalan mutanen da suka mutu, da gwammati da jama'ar kasar ta Masar, tare kuma da bayyana fatan sa na ganin wadanda suka ji rauni sun samu sauki cikin gaggawa.
Hukumomin tsaron kasar Masar sun ba da labarin cewa, wasu 'yan bindiga da ba a san asalinsu ba, sun kai farmaki a jiya Juma'a, kan wasu motocin safa biyu masu dauke da mabiya addinin Krista a yankin Minya dake kudancin kasar.
Rahoton gidan talibijin na kasar ya ruwaito cewa, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla 28, tare da jikata wasu 25. (Bilkisu)