Sisi ya fadi hakan ne a yayin tattaunawa da babban kwamandan rundunar sojin Libya Khalifa Haftar cewa, kasar Masar tana kara nuna goyon bayan cigaba da tattaunawa tsakanin bangarorin kasar ta Libya da basa ga maciji da juna domin samun maslaha don farfadowar zaman lafiya da hadin kan kasar.
Shugaban na Masar ya nanata muhimmancin tabbatar da hadin kai tsakanin dakarun kasar, kana ya nuna bukatar dage takunkumin shigo da makamai da aka azawa kasar, al Sisi ya ce dole ne a dakile hanyoyin samun kudade da na makamai tsakanin kungiyoyin yan ta'adda a kasar.
Da yake karin haske game da al'amurran tsaro a kan iyakar kasar ta yammaci wanda ke makwabtaka da Masar ya ce, kasar na cigaba da gudanar da tarukan tattaunawa a yan watannin da suka gabata domin lalibo bakin zaren magance rikicin siyasa da ya daidaita kasar ta Libya. (Ahmad)