A yayin ganawar, Li Keqiang ya nuna cewa, kasashen Sin da Amurka dukkansu abonkan cinikayya mafi girma ga juna ne, suna cin gajiya iri daya wajen bunkasa tattalin arzikinsu. Tabbas ne za su iya samun moriya iri daya ta hanyar karfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Bangaren Sin yana son kawar da duk wani sabani dake tsakaninsa da bangaren Amurka ta hanyar yin tattaunawa, ta yadda za a iya samun daidaito wajen bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya. Sin kasa ce mai tasowa mafi girma, amma kasar Amurka kasa ce mai arziki mafi girma a fadin duniya, idan sun bunkasa huldar dake tsakaninsu lami lafiya ba tare da tangarda ba, suna kuma kara yin hadin gwiwa da daidaita harkokin dake tsakaninsu yadda ya kamata, ba kawai yana dacewa da moriyarsu kadai ba ne, har ma yana amfanarwa ga kokarin tattabar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwar duniya baki daya.
'Yan majalisun dokokin kasar Amurka sun bayyana cewa, bangaren Amurka yana fatan kasar Sin za ta samu sabon ci gaba, majalisun kafa dokokin kasar Amurka ma suna son kara yin cudanya da kasar Sin. (Sanusi Chen)