in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da mataimakiyar shugaban kwamitin kungiyar EU Mogherini
2017-04-19 11:17:33 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da mataimakiyar shugaban kwamitin kungiyar EU kuma wakiliyar kula da manufofin harkokin waje da tsaro ta kungiyar Federica Mogherini a Zhongnanhai dake nan birnin Beijing a yammacin ranar 18 ga wata.

Li Keqiang ya nuna yabo ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Turai. Ya bayyana cewa, a matsayinsu na manyan bangarori na duniya, ya kamata Sin da Turai sun bayyana ra'ayoyinsu na kiyaye zaman lafiya a duniya da yankuna, da tinkarar kalubalen duniya, kyautata tsarin sarrafa kasa da kasa, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya da samun adalci kan ciniki a duniya, ta haka za a iya tinkarar sauyin yanayin kasa da kasa ta hanyar kiyaye dangantakar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Turai.

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kungiyar EU, da nuna goyon baya ga raya tsarin bai daya a Turai, kana ya yi fatan kungiyar EU za ta kiyaye hadin kai da samun wadata.

A nata bangare, Mogherini ta bayyana cewa, kungiyar EU tana son kara yin hadin gwiwa da warware matsaloli tare da kasar Sin, da sa kaimi ga cimma yarjejeniyar zuba jari a tsakaninsu. Kana tana fatan za a samu kyakkyawan sakamako a gun ganawar dake tsakanin shugabannin Sin da kungiyar EU karo na 19 da za a yi a bana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China