in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin sun baje kolin damammakin ayyukan yi ga daliban jami'ar Masar
2017-05-01 13:25:28 cri
Kamfanonin Sin dake hada hada a Masar, sun gudanar da wani dandali na baje kolin ayyukan yi, ga daliban jami'ar Suez Canal dake lardin Ismailia a gabashin birnin Alkahira.

Kimanin kamfanonin Sin 15 ne, ciki hadda katafaren kamfanin nan na TEDA, da kamfanin gilashi na Jushi, tare da ofishin jakadancin Sin dake birnin Alkahira suka yi hadin gwiwar gudanar da dandalin.

Da yake tsokaci game da hakan ga wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin gudanar dandalin, gwamnan lardin Ismailia Yassin Taher, ya jinjinawa dandalin, da ma tsarin da kamfanonin Sin ke bi wajen samar da guraben ayyukan yi, yana mai cewa jami'ar Suez Canal na da kwararrun dalibai, da ka iya cike dukkanin guraben ayyukan yi da kamfanonin kasar Sin ke bukata.

Dandalin dai ya samu halartar daruruwan dalibai daga sassan ilimi da dama. A hannu guda kuma, kamfanonin Sin sun gabatar da guraben ayyukan yi sama da 300, yayin da kuma dalibai kusan 1,000 suka mika takardun su na neman ayyuka.

Da yake karin haske game da tasirin wannan dandali, Daraktan cibiyar koyar da al'adun kasar Sin ta Confucius a jami'ar ta Suez Canal Zhu Tingting, ya ce kamfanonin Sin dake Masar na bukatar ma'aikata 'yan kasa, matakin da kuma zai samar da guraben ayyukan yi da dama ga Misirawa, wanda hakan zai cika burin da ake da shi na cimma moriyar juna tsakanin sassan biyu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China