in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci kasa da kasa su dakile jan ra'ayin jama'a da kungiyoyin 'yan ta'adda ke yi
2017-05-25 13:52:53 cri
A jiya Laraba ne kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri, inda ya bukaci kasashen duniya da su dauki matakai masu amfani, kuma bisa dokokin kasa da kasa, wajen yaki da jan ra'ayin jama'a da kungiyoyon 'yan ta'adda ke yi.

Cikin kudurin, an bayyana cewa, ya kamata a hana yaduwar dukkan labarai da kungiyoyin ta'addanci suke fitarwa domin shigar da mutane cikin kungiyoyin, da kuma kaddamar da hare-haren ta'addanci cikin kasashen duniya.

Haka kuma, kwamitin ya yi maraba da "tsarin yaki da yaduwar jan ra'ayin jama'a daga kungiyoyin ta'addanci na kasa da kasa" wanda kwamitin yaki da ta'addanci ya gabatar masa a kwanan baya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China