in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci shugabannin addinin Islama a Afrika su shiga cikin yaki da akidar tsattsauran ra'ayi
2017-05-20 13:19:49 cri
Babbar jami'ar MDD a Uganda, Rosa Malanga, ta bukaci shugabannin addinin Islama a Afrika, su shiga cikin yaki da masu kaifin ra'ayin addini, tana mai gargadin da cewa, ci gaba da habakar akidar a nahiyar, zai janyo koma baya ga ci gaban da aka samu.

Rosa Malanga ta ce idan ba a magance matsalar ba, to za ta zama barazana ga ci gaban nahiyar cikin gomman shekaru masu zuwa.

Jami'ar na wannan jawabi ne ga taron malamai da shugabannin addinin Islama daga gabashi da kudancin Afrika, wadanda suka hadu a Uganda don tattauna yadda za a yi yaki da riga kafi tare da magance akidar tsattsauran ra'ayi.

Kungiyar kawance ta addinai dan wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa tare da hadin gwiwar ofishin hukumar raya kasashe ta MDD a Afrika ne suka shirya taron na yini biyu.

Rosa Malango ta ce dole ne shugabannin addini su shiga a dama da su, ta na mai cewa yaki da masu kaifin ra'ayin addin hakkin ne da ya rataya a wuyan kowa.

A nasa bangare, shugaban mabiya addinin Islama a Uganda Sheikh Shaban Mubajie, ya ce hakkin musulmai ne tashi tsaye, su ilmantar da mutane game da addinin, ta yadda za su fahimci cewa ba ya goyon bayan akidar masu tsattsauran ra'ayi.

A karshen taron, shugabanni da malaman addinin, sun amince da samar da wani jadawali da zai ba su damar aiki tare, wajen yaki da dukkan ayyukan da masu akidar ke yi da sunan musulunci.

Sun kuma jadadda sanarwar da shugabanin addinin Islama a yankin yammacin Afrika suka bayar ta nesanta duk wani nau'in tsaurin ra'ayi da sunan Musulunci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China