in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu ruwa da tsaki a nahiyar Afirka na taro game da hanyoyin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda
2017-04-04 12:50:20 cri

Mataimakin shugaban kasar Sudan Hassabo Mohamed Abdul-Rahman, ya bayyana ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda, da na masu dauke da makakai, da ma wasu daga kungiyoyi masu zaman kan su, a matsayin kalubale, da ya kamata kasashen Afirka su yi hadin gwiwar yaka.

Mr. Abdul-Rahman wanda ke yin wannan kira a birin Khartoum a jiya Litinin, yayin wani taron jami'an tsaron farin kaya na kasashen nahiyar, da sauran masu ruwa da tsaki, ya ce kungiyoyin masu dauke da makamai, da mayakan sa kai na kasa da kasa, da wasu kungiyoyi na masu zaman kan su marasa amfani, na haifar da mummunan tasiri ga tsaro da daidaito a nahiyar Afirka.

Mataimakin shugaban kasar na Sudan ya kara da cewa, ya zama wajibi masu ruwa da tsaki a fannin tsaro na Afirka, su hada karfi da karfe wajen tunkarar wannan kalubale, ta hanyar musayar kwarewa, da tsare tsaren ayyuka. Ya ce sau da dama 'yan ta'adda ba kasa ce a gaban su ba, domin kuwa sun fi maida hankali ga cutar da al'ummu marasa kariya, kamar fararen hula, da wadanda suke tsarewa, tare da jami'an bada agajin jin kai.

A cewar sa laifukan da irin wadannan kungiyoyi ke aikatawa, sun fi shafar harkokin mallakar kudade, da sauran wadanda aka haramta karkashin dokokin kasa da kasa.

Taron na masu ruwa da tsaki game da harkokin tsaro dai ya samu halartar wakilai daga kasashen Afirka su 27, da wakilan shiyya shiyya da na hukumomin kasa da kasa. Sai kuma jami'an kungiyar AU da manazarta, da wakilan cibiyoyin binciken dake nahiyar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China