in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Jamus na neman wani dan Tunisiya kan harin Berlin
2016-12-22 11:00:24 cri

Rahotanni daga kasar Jamus sun ce, 'yan sandan kasar suna cigiyar wani dan asalin kasar Tunisiya dake gudun-hijira a Jamus, bisa zarginsa da kai hari wata kasuwar Kirismetti a birnin Berlin.

Rahotannin sun ce, 'yan sandan sun gano takardun shaida a cikin motar da mutumin mai Suna Anis Amri dake tsakanin shekaru 21 zuwa 23 ya tuka, inda suka gano ya taba amfani da sunaye da takardun fasfo na karya da yawa.

Anis Amri, ya shiga kasar Italiya a shekara ta 2012, kuma tun daga watan Yulin shekarar 2015, ya fara zama a kasar Jamus.

Rahotanni sun ce Amri ya nemi mafaka daga gwamnatin Jamus a watan Afrilun shekarar da muke ciki, sai dai har yanzu ba'a ba shi izini ba.

A watan Agustan shekarar 2016 ne kuma, aka kama shi a birnin Friedrichshafen dake kudancin kasar Jamus, a lokacin yana rike da takardar izinin zama a kasar Italiya.

A wani labarin kuma, rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar Anis Amri na karkashin wata kungiyar masu tsattauran ra'ayi a kasar Jamus, wadda ta fara kulla makarkashiyar kai hari kan kasar tun shekara ta 2015. Bugu da kari, A watan Nuwamba bana ne 'yan sandan Jamus suka cafke madugun wannan kungiya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China