Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana jiya Talata cewa, hanyar siyasa ita ce hanya daya kawai da za a warware batun Sudan ta Kudu. Don haka., kamata ya yi kasashen duniya su sa kaimin bangarori daban daban na kasar Sudan ta Kudu da su yi watsi da duk wasu matakan soja, kana su koma hanyar siyasa don warware batun cikin hanzari.
Wu Haitao ya yi jawabi a taron da kwamitin sulhun MDD ya shirya game da batun Sudan ta Kudu cewa, don amsa kiran MDD, gwamnatin kasar Sin ta tsaida kudurin samar da kudi dala miliyan 5 ga kasar Sudan ta Kudu ta hannun shirin samar da abinci na duniya, tare da samar da gudummawar hatsi ton kimanin 8750 don taimakawa kasar Sudan ta Kudu don tinkarar matsalar yunwan da ta ke fama da ita. (Zainab)