Kakakin Jam'iyyar SPLM Bol Makueng, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Sudan ta Kudu za ta koya daga kasar Sin, yadda ta yi nasarar sauya kanta zuwa kasa mai karfi a duniya.
Bol Makueng ya jinjinawa rawar da kasar Sin ke takawa, wajen taimakawa wanzuwar zaman lafiya da ci gaba a Sudan ta Kudu, ya na mai cewa, gwamnati za ta hada hannu da Sin a fannonin da suka hada da raya karkara da fasaha da samar da kayakin more rayuwa.
Ya ce a shirye Sudan ta Kudu ta ke, ta hada hannu, ba kadai da Kasar Sin ba, har ma da sauran kasashe, muddin dai za a amfana daga hadin gwiwar. (Fa'iza Mustapha)