Rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake aiki a kasar Congo (Kinshasa), ta tabbatar da cewa, a jiya Talata, wasu 'yan gudun hijira na kasar Sudan ta Kudu sun yi garkuwa da ma'aikatan MDD su 16, a sansanin MDD da ke kusa da birnin Goma, babban birnin lardin Nord-Kivu dake kasar Congo (Kinshasa). Amma daga bisani an saki wadannan ma'aikatan MDD baki daya. Kuma yanzu haka sansanin yana karkashin kulawar sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD. (Tasallah Yuan)