Rahotanni sun ce a daddaren ranar 3 ga wata ne aka kai hari kan tawagar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu a garin Leer dake jihar Unity.
Sai dai, Sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Ghana dake sansanin sun mayar da martani tare da cimma nasarar fatattakar maharani.
Har yanzu ba a tabbatar da asalin wadanda suka kai harin ba, duk da cewa babu wani sojan da ya rasa ransa ko ya jikkakata yayin harin.
Sanarwar da kwamitin ya bayar a jiya ta bayyana cewa, za a shigar da duk wanda ya kai hari kan sojojin kiyaye zaman lafiya ko ma'aikatan jin kai kai tsaye ko ba kai tsaye ba, cikin jerin sunayen da za a kakabawa takunkumi.
Kana kwamitin sulhun ya yi Allah wadai da rikice-rikicen da ake samu a kasar Sudan ta Kudu, yana mai kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa su kiyaye yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, tare da kawar da duk abubuwan dake cikas ga ayyukan jin kai. (Zainab)