Sanarwar da ofishin ya fitar a jiya ta ce, a ranakun 10 da 11 ga wata, wato lokacin da yake halartar taro kan Somaliya a birnin London, Mr. Guterres ya tattauna da shugaban kungiyar IGAD kuma firaministan kasar Habasha Hailemariam Dessalegn, da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni da kuma shugaban kwamitin kungiyar AU Moussa Faki da wasu manyan shugabannin kan halin da kasar Sudan ta Kudu take ciki a yanzu.
Kuma yayin tattaunawarsu kan wannan batu, Mr. Guterres ya nuna damuwarsa matuka, kan yanayin tsaro da yanayin jin kai a kasar, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasashen dake yankin da gamayyar kasa da kasa, su hada hannu wajen warware matsalar, musamman ma ta hanyar dakatar da bude wuta, ta yadda za a iya samar da taimakon jin kai, da kuma ba tawagar musamman da aka tura kasar damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Har ila yau, ya yi kira da a warware matsalar a siyasance ta yadda zai samu karbuwa da amincewa tsakanin al'ummar kasar tare da kawo karshen rikicin. (Maryam)