in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari kan motoci biyu a kasar Sudan ta Kudu
2017-05-08 10:43:44 cri
Wani jami'in gwamnatin Sudan ta Kudu ya tabbatar a jiya Lahadi cewa, dakaru sun kai hari kan motoci biyu masu dauke da fasinjoji dake kan hanya daga birnin Juba zuwa Bor dake jihar Jonglei ta tsakiyar kasar, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 21 tare da raunata wasu 25.

Ma'aikatar watsa labaru ta jihar Jonglei ta tabbatar da cewa, an dakatar da motocin biyu a wata tashar binciken ababan hawa da ba ta aiki a yanzu da, mutanen da suka mutu da wadanda suka raunata a sakamakon harin sun hada da mata da kananan yara.

A halin yanzu, ba a san dalilin da ya sa aka kai harin ba, hukumar da abin ya shafa tana gudanar da bincike kan batun. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China