Hukumar ta bayyana cikin sanarwar da ta fiddar cewa, ta wadannan matakai, kungiyar EU za ta karfafa dokokinta na yaki da halalta kudin haram, hana kai-komin kudin da aka samu ba bisa doka ba, da kuma rike kudade da kadarorin da aka samu ba bisa doka ba, ta yadda za a hana 'yan ta'adda samun kudade ta kowa ce hanya.
Hanya daya ta yin riga kafin aukuwar hare-haren ta'addanci, ita ce yin bincike da kuma toshe hanyoyin shigar kudaden da ba a san daga inda suka fito ba.
A sa'i daya kuma, hukumar zartarwar kungiyar ta EU ta fidda wata sabuwar dokar yaki da halalta kudin haram, domin hana masu aikata wannan laifi cimma burinsu ta hanyar yin amfani da bambancin manufofin tsakanin mambobin kungiyar, ta yadda za a warware matsalolin da abin ya shafa sakamakon bambancin shari'a da dokokin 'yan sanda a tsakanin kasa da kasa.
Ban da haka kuma, kungiyar EU za ta kara yin bincike kan abubuwan da suka shafi kudade masu dimbin yawa. A nan gaba, za a hana mutane shiga ko kuma fita da tsabar kudin Euro sama da dubu 10 daga kasashen kungiyar EU. (Maryam)