in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na Mali
2017-05-22 11:25:17 cri
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana a jiya Lahadi, da takwaransa na Mali Abdoulaye Diop a Bamako, babban birnin kasar Mali.

A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya ce, kasar Sin na son taimakawa kasar Mali, wajen farfado da tsarin masana'antunta, ta yadda za ta karfafa karfinta na dogaro da kanta, da samun 'yanci a fannin tattalin arziki.

A nasa bangaren, Abdoulaye Diop ya bayyana cewa, kasar Mali ta amince da ra'ayin kasar Sin na zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Ministocin biyu sun kuma yi shawarwari kan wasu batutuwan da suka shafi kasa da kasa da kuma shiyyoyi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China