Cikin jawabinsa, Wang Yi ya bayyana cewa, ana ci gaba da fuskantar sauye-sauyen yanayi a fannoni daban daban a duniya, gamayyar kasa da kasa suna sa ran kasar Sin za ta iya ba da gudummawa kan harkokin kare zaman karko da neman ci gaba na kasa da kasa. Haka kuma, kasar Sin tana son sauke nauyin dake wuyanta na ba da gudumawarta cikin himma da kwazo kamar yadda ya kamata, amma ba ta taba yin tunanin cewa, za ta ba da jagoranci kan kasa da kasa ba.
Kasar Sin tana son kulla dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasa da kasa bisa ka'idojin nuna adalci da kuma bude kofa ga waje, yayin da gaggauta gina sabuwar dangantaka da za ta sa a cimma moriyar juna, lamarin da zai ba da taimako wajen cimma burinmu na samun dunkulewar bil Adama.
Bugu da kari, ya ce, kasar Sin za ta karfafa dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasashe masu tasowa, domin ba da taimko da goyon baya ga juna a yayin da aka dukufa wajen neman bunkasuwa. (Maryam)