Ministan harkokin waje na kasar Sin ya tattauna tare da takwaransa da kasar Birtaniya
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna da takwaransa na kasar Burtaniya Boris Johnson ta wayar tarho a jiya Litinin, inda suka yi musayar ra'ayi kan batun Syria da kuma halin da ake ciki a zirin Koriya. Gaba daya Ministocin na ganin cewa, a lokacin da ake cika shekaru 45 da kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen biyu, ya kamata su rubanya kokari wajen daukaka huldar da ke tsakaninsu zuwa wani sabon mataki. (Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku