Ministocin Sin da Birtaniya sun tattauna kan batun nukiliya na Koirya ta Arewa
A ranar Jumma'a ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaran aikinsa na kasar Birtaniya Boris Johnson yayin da yake halartar taron ministoci da kwamitin sulhun MDD ya shirya kan batun nukiliyan zirin Koriya, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan batun. A ganinsu, halin da ake ciki a zirin Koriya ya tsananta, akwai yiwuwar fuskantar hadarin rikici a zirin. A don haka ne kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taron ministocin. Kamata ya yi bangarori daban daban da abin ya shafa su tsaya tsayin daka kan manufar kawar da makaman nukiliya a zirin, da aiwatar da kudurin kwamitin sulhun MDD game da batun, da hana Koriya ta Arewa gudanar da shirinta na gwajin makamai masu linzami, kana ya kamata a yi shawarwari don sa kaimi ga warware batun cikin lumana, in ji jami'an 2. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku