A yayin ganawar da ta gudana a jiya Juma'a, Shugaba Abdel Aziz ya ce, kasarsa na girmama dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, ta na kuma godiya kan goyon baya da tallafin da kasar Sin ke samar mata.
A cewar shugaban, saurin bunkasar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na kawo moriya ta hakika ga jama'ar Mauritania, kuma har kullum, kofarsu a bude ta ke ga kasar Sin.
Baya ga haka, ya bayyana cewa, kasarsa na mai da muhimmanci a kan matsayi da kuma rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin kasa da kasa, inda ya ce ta na goyon baya da kuma shiga ayyuka bisa shawarar "Ziri daya hanya daya" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar. Sannan za ta karfafa hadin kai tare da Sin kan wasu batutuwa, don kiyaye moriyar kasashe masu tasowa musamman ma kasashen Afirka.
A nasa bangaren, Wang Yi ya ce, kasar Sin na goyon bayan kasar Mauritania wajen bin hanyar samun ci gaba da ta dace da yanayin da take ciki.
Har ila yau, ya ce kasar Sin na kara ba kamfanoninta kwarin gwiwar zuba jari a Mauritania, da nufin taimaka mata ta fuskar raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma, har ma da kafa tsarin masana'antu da ta iya dogara a kai don neman ci gaba da kanta.
A cewar Wang, a ko da yaushe, kasar Sin na amfani da kujerarta ta dindindin a kwamitin sulhun MDD, wajen goyon bayan kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka. (Bilkisu)