in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Mali ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2017-05-22 11:23:10 cri

Jiya Lahadi, a madadin shugaban kasar Mali wanda a halin yanzu yake halartar taron a ketare, firaministan kasar Mali Abdoulaye Idrissa Maiga ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a babban birnin kasar, Bamako.

A yayin ganawar tasu, malam Maiga ya bayyana cewa, kasar Mali tana mai da kasar Sin muhimmiyar abokiyarta bisa manyan tsare-tsare, ya kuma nuna godiya matuka domin taimako da goyon bayan da kasar Sin ta samarwa kasarsa, musamman ma a fannin inganta tsaro da yanayin zaman lafiya na kasar Mali.

Ya kuma kara da cewa, kasar Mali tana mai da hankali sosai kan hadin gwiwar dake tsakninta da kasar Sin kan harkokin dake shafar kasa da kasa, kuma tana fatan kasar Sin za ta iya taimaka mata wajen kiyaye zaman lafiyar kasar da kuma yaki da ta'addanci. Sa'an nan, kasar Mali za ta ci gaba da yin shawarwari da hadin gwiwa da kasar Sin a fannin kwaskwarimar kwamitin sulhu na MDD.

A nasa bangare, Wang Yi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Mali wajen kare mulkin kanta da kuma dunkulewar kasar baki daya, tana fatan kasar Mali za ta iya samun hanyar bunkasuwar kasa dake dacewa da halin da kasar take ciki, yayin da yaki da ta'addanci yadda ya kamata.

Haka zalika, ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka da su warware matsalolinsu ta hanyoyin da suke son, za ta kuma ci gaba da kiyaye ikon kasashen Afirka cikin kwamitin sulhu na MDD.

Kasar Mali ita ce kasa ta uku da minista Wang ya kai ziyara bayan kasar Mauritania da kuma kasar Cape Verde, cikin ziyararsa a yammacin kasashen Afika na wannan karo, sa'an nan, a yau Litinin, Mr.Wang zai ziyarci kasar Coate d'Ivoire. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China