Yayin ganawar da ta gudana a jiya, Wang yi ya bayyana kasashen Sin da Mauritania a matsayin kawayen juna. Inda ya ce kasancewar Mauritania mamba a dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka, da kuma dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Larabawa, tana iya amfani da wadannan dandamalin biyu wajen karfafa hadin kai da kasar Sin a dukkan fannoni, kuma Kasar Sin ta yi imanin cewa Mauritania na da kyakkyawar makoma.
Baya ga haka, ministan harkokin wajen na Sin ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin na goyon bayan kasashen Afirka wajen warware matsalolinsu da kansu, inda ta ke goyon bayan muhimmiyar rawar da kungiyoyin shiyyar ke takawa kan harkokin da suka shafi kasashensu.
A nasa bangaren, mista Izid Bih ya bayyana cewa, kasar Mauritania na son koyi da fasahohin da Sin ta yi amfani da su wajen samun ci gaba, tare kuma da karfafa hadin kai da moriyar juna a fannoni daban- daban.
Baya ga haka, ministocin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan muhimman batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka. (Bilkisu)