Mr. Wang Yi ya jaddada cewa, dukkan kudurorin da kwamitin sulhun MDD ya gabatar na kunshe ne cikin fannoni biyu. Na farko shi ne nuna adawa da manufar kasar Koriya ta Arewa ta mallakar makaman nukiliya, da daukar matakan hana kasar kera makamai masu linzami na nukiliya. Na biyu shi ne jaddada warware batun cikin lumana, da magance daukar matakan da ka iya tsananta halin da ake ciki, da ci gaban shawarwari a tsakanin bangarori shida cikin hanzari.
Ya ce kamata ya yi a aiwatar da kudurin kwamitin sulhun a dukkan fannoni, ba wai kawai biyan bukatun wasu bangarorin su kadai ba. A cewarsa gwajin makamai masu linzami na nukiliya ya sabawa kudurin kwamitin sulhun, amma yin atisayen soja a zirin Koriya, shi ma bai dace da manufar kudurin ba.
Wang Yi ya ce, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, da kafa tsarin zaman lafiya a zirin. A hannu guda Sin na fatan ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen cimma wadannan burika. (Zainab)