Yayin ganawar ta su a jiya Jumma'a, ministocin biyu sun nuna cewa, halin da ake ciki yanzu a zirin Koriya na kara ta'azzara, a don haka, ya zama tilas kwamitin sulhun MDD ya kira wannan taro.
Bangarori daban-daban sun amince cewa, halin da ake ciki yanzu a zirin Koriya na fuskantar babban kalubale, kuma sun jaddada burinsu na kawar da makaman nukiliya baki daya, suna masu alkawarta cewa, za su yi kokarin aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun, da daidaita matsalar ta hanyar tattaunawa, a wani kokari na sassauta halin da ake ciki yanzu a zirin Koriya.(Murtala Zhang)