Wang Yi ya ce, kasar Sin na lale marhabin da Guterres don ya halarci babban dandalin tattauna kan shirin 'ziri daya hanya daya' tsakanin kasa da kasa, wanda za'a yi a watan Mayun bana a birnin Beijing.
Wang ya ce, kasar Sin na fatan wannan dandali zai samar da wata alama ga kasashen duniya dake nuna cewa, Sin na son yin hadin-gwiwa da cimma moriya tare da sauran kasashe.
Kana, kasar Sin na son yin amfani da wannan dama, wajen inganta hadin-gwiwa da MDD da ma sauran masu ruwa da tsaki, a fannonin neman ci gaba mai dorewa da tunkarar matsalar sauyin yanayi da sauransu.
A nasa bangaren, Antonio Guterres ya ce, yana fatan halartar wannan muhimmin dandalin tattaunawa, yana mai cewa, kasar Sin na nuna cikakken goyon-bayanta ga MDD da bayar da babbar gudummawa a fannoni da dama, ciki har da yin ciniki cikin 'yanci a fadin duniya, da wanzar da zaman lafiya, da kuma neman ci gaba da raya harkokin duniya.
Antonio Gutteres ya ce MDD na maida hankali sosai wajen hada hannu da kasar Sin, musamman game da wasu muhimman shirye-shiryen da gwamnatin kasar ta fitar, ciki har da shirin ziri daya hanya daya, da kafa bankin zuba jari na Asiya.
MDD na fatan Sin za ta kara taka rawar gani a batutuwan da suka shafi duniya baki daya.(Murtala Zhang)