Cikin sharhin, ta yi bayani cewa, cikin 'yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ta kara zuba jari a fannin masana'antun kira a kasashen Afirka. Kuma bisa kididdigar da aka yi, an ce, cikin ko wace shekara, kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu suna zuba jari sama da sau 150 a nahiyar Afirka kan ayyuka da dama dake shafar fannin kira, lamarin da ya ba da muhimmiyar gudummawa wajen raya harkokin masana'antu a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a kasashen Afirka sun ba da taimako ga kasashen Afirka wajen neman bunkasuwar masana'antu da kuma kawar da talauci a kasashensu. Sabo da tsarin ya samar da karin guraben ayyukan yi a kasashen, bisa labarin da aka samu, an ce, ma'aikata kashi 78 bisa dari dake cikin kamfanonin kasar Sin dake nahiyar Afirka mazaunan kasashen ne, a wasu kamfanonin kuma, adadin ma'aikata mazaunan wurin ya kai kimanin kashi 99 bisa dari.
Haka kuma, kamfanonin kasar Sin dake nahiyar Afirka sun ba da gudummawa wajen shirya horaswa ga al'ummar kasashen, musamman ma ga matasa, bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kamfanonin wurin, ta yadda za su zama masu kwarewa a fannin ciniki, sa'an nan za su ba da muhimmin taimako wajen raya harkokin masana'antu da cinikayya a nahiyar Afirka. (Maryam)