in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jacob Zuma ya gana da mataimakiyar firaministan Sin
2017-04-26 19:55:47 cri
A jiya Talata ne, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya gana da mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, wadda a yanzu haka ke ziyarar aiki a kasar da kuma halartar taron farko na tsarin cudanyar al'adu a tsakanin Sin da Afirka ta kudu.

A yayin ganawar, shugaba Zuma ya bayyana cewa, yana farin ciki ganin yadda aka tabbatar da daidaiton da ya cimma tare da shugaban kasar Sin Xi Jinping game da kafa tsarin cudanyar al'adu a tsakanin kasashen biyu cikin sauri. Yana mai cewa, gudanar da tsarin zai shigar da jama'ar kasashen biyu mafi yawa a yunkurin bunkasa dangantakar dake tsakanin Afirka ta kudu da Sin, kana za su ci gajiyar sakamakon bunkasuwar dangantakar.

A nata bangaren madam Liu Yandong ta bayyana cewa, an cimma nasarar shirya taron karon farko na tsarin, inda aka tsara shiri kan muhimman fannonin da kasashen biyu za su hada kai da yin cudanya a kai a nan gaba. Kasar Sin na fatan hada kai tare da Afirka ta kudu don ciyar da cudanya da hadin kan al'adun kasashen biyu gaba, kana da inganta harsashin sada zumunci a tsakanin Sin da Afirka da kudu, da kuma Sin da kasashen Afirka ta fannonin ra'ayin jama'a da al'umma. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China