A yau Litinin 24 ga wata ne, mataimakiyar firaministan kasar Sin madam Liu Yandong ta halarci taron farko na tsarin musayar al'adu tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu a birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu.
A jawabinta yayin taron, madam Liu ta ce, tun bayan Sin da Afirka ta Kudu suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu a shekarar 1998 har zuwa yanzu, kasashen suna ci gaba da raya huldarsu daga dukkan fannoni. Yanzu jimillar kudaden da suka samu a fannin ciniki a tsakanin juna ta kai dalar Amurka biliyan 35.3, kuma kasar Sin ta zama abokiyar cinikayya mafi girma ta Afirka ta Kudu cikin shekaru 8 a jere. Haka kuma, Sin da Afirka ta Kudu dukkansu mambobi ne na kasashen BRICS, kungiyar G20, suna kuma ba da gudummowa wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, da kuma tsakanin kasashe masu tasowa, da tafiyar da harkokin kasa da kasa. Huldar da ke tsakaninsu ta zama wani kyakkyawan misali ta fannin hadin kai a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da ma kasashe masu tasowa baki daya. (Tasallah Yuan)