in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jimillar cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ta karu da 16.8% a farkon watanni uku na bana
2017-05-11 13:57:12 cri

Bisa alkaluman da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar yau Alhamis, an ce, jimillar cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ta kai Dalar Amurka biliyan 38.8 a farkon watanni uku na shekarar bana, wadda ta karu da kashi 16.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.

A fannin zuba jari ma, yawan kudin da kamfanonin kasar Sin ta zuba a Afirka ba ta fannin hada-hadar kudi ba ya karu da kashi 64 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, har ma adadin kudin ya zarce Dala miliyan 750. A ciki, matsakaicin yawan kudin da kasar Sin ta zuba wa kasashen Najeriya, Zambia, Kenya, Habasha, da Uganda ya zarce dala miliyan 50.

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Sun Jiwen ya fada cewa, ganin yadda hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin tattalin arziki da cinikayya ya samu karuwa sosai, ana sa ran cewa, hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu zai ci gaba da samun kyautatuwa, har ma zai kai wani sabon mataki.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China