in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da kasashen Afirka sun tattauna game da hadin kai wajen yaki da cinikin namun daji
2017-05-04 19:09:54 cri
A jiya Laraba 3 ga watan nan ne aka gudanar da taron shekara-shekara, na kungiyar tattaunawa game da dokoki tsakanin nahiyoyin Asiya da Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya, taron da aka yiwa lakabin "hada kai domin yaki da haramtaccen cinikin namun daji, da tsire-tsire bisa dokokin kasa da kasa".

Shugaban sashen kula da ka'idoji da dokoki na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Xu Hong, ya jinjinawa gudummawar da yarjejeniyar hana ciniki da namun daji da tsirrai dake daf da karewa ta kasa da kasa wato CITES ke bayarwa, da hadin gwiwa da sauran tsare-tsare na dokokin kasa da kasa, da hukumomin MDD masu ruwa da tsaki a wannan fanni, wajen tabbatar kariya ga namun daji da tsirrai, tare da yaki da haramtaccen cinikin su.

Mr. Xu ya kuma jaddada cewa, wannan aiki kalubale ne da kasa da kasa suke fuskanta tare, don haka ake bukatar kara yin hadin gwiwa, da daukar matakai, da tinkarar batun yadda ya kamata.

Ministan kula da yanayi da albarkatun halittu na kasar Kenya, da minisan dokoki da harkokin tsarin mulki na kasar Tanzaniya, da babban sakataren kungiyar shawarwari game da dokoki ta Asiya da Afirka, su ma sun yabi gwamnatin kasar Sin, bisa muhimmanci da take dora, kan sha'anin kare gandun daji da tsirrai, musamman ma batun ayyana dakatar da samar da sayan da ake yi da hauran gwiwa a cikin kasar, kafin karshen shekarar 2017. A ra'ayin wadannan jami'ai, wannan manufa ta shaida nauyin da kasar Sin ke saukewa a sha'anin duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China