in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin kasar Sin sun nuna fasahohi a bikin makon wutar lantarki na Afirka
2017-05-17 13:38:30 cri
An kaddamar da bikin makon wutar lantarki na Afirka na shekarar 2017 a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu a jiya Talata. Bikin wanda ya kasance bajekoli mafi girma a fannin fasahohin wutar lantarki a nahiyar Afirka, ya janyo hankalin kamfanoni fiye da 300 na kasashe fiye da 80, ciki har da kamfanonin kasar Sin da dama.

A wajen bikin kaddamarwa, mataimakin minista mai kula da kamfanonin mallakar gwamnati na kasar Afirka ta Kudu Dikobe Martins, ya yi tsokaci da cewa, nahiyar Afirka na fama da matsalar karancin wutar lantarki mai tsanani. Saboda haka, ba za a samu ci gaba mai dorewa a nahiyar ba, matukar ba a shawo kan matsalar lantarki ba.

Jami'in ya ce, ya kamata kasashen da ke nahiyar Afirka, da gamayyar kasa da kasa, su dora cikakken muhimmanci kan yunkurin warware wannan matsala.

Duk a wajen taron, bankin duniya ya ba da wani rahoto kan yanayin da kasashen Afirka suke ciki a fannin lantarki, inda ya ce, yawancin kamfanonin wutar lantarki dake Afirka, suna gudanar da ayyukansu ne bisa cin bashi. Ganin haka ya sa wasu kwararru na bankin a fannin makamashi ke cewa, dole ne a yi kokarin taimakawa kamfanoni, domin su samu damar lura da kansu. Sabanin hakan kuwa zai kara jefa su cikin kangin bashi ba kakkautawa, kuma a karshe za su shiga mawuyacin hali. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China