in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakiyar Firayiministan kasar Sin ta jaddada muhimmiyar rawar da matasa ke takawa ga dangantakar kasar Sin da Afrika
2017-04-27 15:06:00 cri
Mataimakiyar Frimiyar kasar Sin dake ziyara a Afrika Liu Yandong, ta jaddada muhimmancin rawar da matasa ke takawa wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Nahiyar Afrika.

Da take jawabi yayin rufe bikin matasan Sin da Afrika karo na biyu a kasar Afirka ta Kudu, Liu Yandong ta ce tun fil- azal, matasa na ta ka muhimmiyar rawar wajen habaka dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Nahiyar Afrika.

Ta kuma bayyana fatan cewa, matasan bangarorin biyu, za su alkinta abota da alakar da aka kulla yayin bikin, tare da taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa daddadiyar dangantaka dake tsakanin Sin da nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China