in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta shirya taron ministoci na kawancen kasa da kasa game da murkushe IS
2017-03-10 11:23:28 cri
Jiya Alhamis, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta ce, sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson ne zai shugabanci taron ministocin kawancen kasa da kasa na murkushe kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS.

Manufar Taron wanda zai gudana a ranar 22 ga wata a birnin Washington, ita ce, tattauna matakan da za a dauka na murkushe kungiyar.

Wata sanarwar da majalisar ta bayar, ta ce ministocin harkokin waje da manyan jami'an kasashe mambobin kawancen ne za su halarci taron. Wannan dai, zai kasance cikakken taro irinsa na farko da kawancen ya shirya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China