Jaridar Ahram ta kasar ta wallafa a shafinta na Intanet cewa, wasu mahara da ba a san ko su waye ba, sun kai farmaki shingen binciken jami'an tsaro, amma babu abun da ya samu limaman dake cikin mujami'ar.
An dai garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Sham El-Sheikh.
Wannan harin na zuwa ne kwanaki bayan an kai hare-hare biyu kan wasu mujami'u a kasar, alamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 47, kuma kungiyar IS ta dauki alhakinsa.
Masar dai na fama da hare-hare kan jami'an tsaro a yankin arewacin Sinai, inda Kungiyar IS ta fi kai farmaki, al'amarin da ya hallaka daruruwan jami'an tsaro. (Fa'iza Mustapha)