in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pentagon: Hare hare kan dakarun IS ya hallaka fararen hula a kalla 352
2017-05-01 12:47:10 cri
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta ce a kalla fararen hula 352 ne suka rasa rayukan su, sakamakon hare haren da dakarun hadin gwiwa wanda Amurka ke jagoranta suka kai, kan mayakan kungiyar IS a kasashen Iraqi da Syria, tsakanin watan Agustan shekarar 2014 zuwa watan Maris na bana.

Cikin rahoton wata-wata da ma'aikatar ke gabatarwa, game da yawan fararen hula da ke rasa rayukan su sakamakon hare haren sojin, Pentagon ta ce tana nazartar wasu rahotanni game da kisan karin wasu fararen hular su 42.

Bisa alkaluman da hukumar ta fitar, akwai fararen hula 45 da suka rasa rayukan su, tsakanin watan Nuwambar bara zuwa watan Maris na Bana. Kana wasu mutane 80 sun gamu da ajalin su, tsakanin watan Agustan shekarar 2014 zuwa bana, wadanda a baya ba a ambata ba.

Sai dai kuma alkaluman na Pentagon sun saba wa wanda ofishin kungiyar Amnesty International mai ofishi a birnin Landan ya fitar, wanda ya ce yawan fararen hular da dakarun Amurka suka hallaka cikin hare hare 11 da suka kaddamar a Syria kadai, ya kai mutum 300. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China