Wata sanarwa da rundunar sojin Syria ta fitar jiya, ta ce rundunar kawancen ta kai harin ne tsakanin karfe 5:30 da karfe 5: 50 na yammacin ranar Laraba, a ma'ajiyar makamai na kungiyar IS dake lardin Deir ez-Zor na gabashin kasar.
Ta ce, hayakin da ya tashi sakamakon fashewar boma-boman ya sauya launi zuwa rawaya, sabo da fitar iska mai guba, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane da dama.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, wannan ya nuna cewa, kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi da suka hada da kungiyar IS da kungiyar Jabhat Fateh Al-Sham sun mallaki makamai masu guba.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa, kakakin rundunar kawancen John Dorrian, ya musanta ikirarin na rundunar sojin Syria, yana mai cewa rundunarsu ba ta kai harin ba. (Maryam)