Bisa rahoton da aka fidda mai taken "nazari kan harkokin zuba jari a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka", an ce, adadin jarin da kasar Sin ta zuba ga kasar Amurka gaba daya, ya kai dallar Amurka biliyan 46 a shekarar 2016, wanda ya ninka sau uku idan an kwatanta da na shekarar 2015. Kana adadin jarin da kasar Amurka ta zuba wa kasar Sin bai karu sosai ba.
Haka kuma, an ce, fannonin da bangarorin biyu suka zuba jari kai tsaye cikin su a shekarar 2016 sun karu sosai. Kuma akwai fannoni guda biyar da suka hada da kadarar gidaje, da fannin sufuri da ginin ababen more rayuwa, da fasahohin sadarwa, da kayayyakin masarufi da na ba da hidima, da kuma fannin nishadantarwa da kafofin watsa labarai, wadanda adadin jarin da aka zuba a cikin ko wanensu ya wuce dallar Amurka biliyan 5. (Maryam)