Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya bullo da wani rahoto game da batun kare hakkin dan Adam na shekara ta 2016 da Amurka ta fitar, inda ya ce, a shekarar 2016, mu'amalar da ke tsakanin al'ummomin kasar Amurka ta kara yin tsami. 'Yan sandan kasar fararen fata su kan harbe Amurkawa 'yan asalin Afirka, ana kuma nuna wariyar launin fata a harkokin shari'a. Kana akwai bambanci a tsakanin 'yan kananan kabilu da fararen fata ta fuskar kudin shiga da samun aikin yi. Ana kuma nuna wariyar launin fata a makarantu da ma zamantakewar al'umma. Haka kuma yawan Amurkawa 'yan asalin Afirka da 'yan sandan kasar suka harbe su ya ninka yawan Amurkawa fararen fata da 'yan sandan suka harbe sau 2.5. (Tasallah Yuan)